Mutum ɗaya ya rasu, yayin da wasu huɗu suka jikkata sakamakon rushewar wani gini da ya faru a titin Sultan dake Nasarawa GRA cikin birnin Kano a ranar Juma’a.
Babban sakataren hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Kano (SEMA), Alhaji Isyaku Lawan Kubarachi, ya ce mutane biyar ne aka ceto daga ƙarƙashin ginin sakamakon haɗin gwiwar jami’an ceto da al’umma. Sai dai abin takaici, ɗaya daga cikin waɗanda aka ceto ya rasu saboda munanan raunukan da ya samu.
Ya kuma yi kira ga masu gine-gine da al’umma da su riƙa bin ƙa’idojin gine-gine tare da tabbatar da cewa ƙwararrun injiniyoyi ne ke kula da duk wani aikin gini domin kauce wa irin wannan ibtila’i.
Haka kuma ya isar da saƙon ta’aziyyar Gwamnatin jihar Kano ga iyalan mamacin, tare da yi wa waɗanda suka jikkata addu’ar samun sauƙi cikin gaggawa.




Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t