Ibtila’i: Gobara ta tashi a otal mai ɗauke da alhazan Nijeriya 484

FB IMG 1749374643790

Hukumar Alhazai ta Ƙasa,  NAHCON, ta tabbatar da gobara a wani otal mai ɗauke da alhazan Nijeriya 484 da ke titin Shari Mansur a birnin Makkah.

Alfijir labarai ta ruwaito NAHCON, sanarwa daga Kakakin ta, ta ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 12 na rana a agogon saudiyya a yau Asabar.

Ta ce alhazan da ke zaune a otal din, mai suna Imaratus Sanan na ɗauke da alhazai ne da su ka zo Hajji ta kamfanoni masu zaman kansu.

Sai dai kuma duk da fargabar da aka shiga, hukumar NAHCON ta ce ba a sami asarar rayuka ko jikkata ba, kuma an kwashe dukkan alhazan lafiya zuwa garin Mina.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Hukumar NAHCON ta tabbatar da cewa daukacin alhazan Najeriya 484 da gobara ta shafa a otal dinsu da ke titin Shari Mansur a Makkah suna cikin koshin lafiya.

Bayan afkuwar lamarin, Shugaban Hukumar NAHCON, Farfesa Abdullahi Usman, tare da rakiyar Kwamishinonin hukumar sun ziyarci wurin.

Da ya ke nuna damuwa yayin ziyarar, Farfesa Abdullahi ya ba da umarnin mayar da alhazan da abin ya shafa cikin gaggawa zuwa wani sabon masauki.”

Ya kuma jajanta wa alhazan da abin ya shafa, yana mai tabbatar da cewa hukumar za ta ba da duk wani tallafi da suke bukata.

NAHCON ta kuma yaba da matakin gaggawar da hukumar bayar da agajin gaggawa ta Saudiyya ta dauka da hadin kan ma’aikatan otal wajen Shawo kan lamarin.

Ga Masu Son Bada Talla A Kira   +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zN

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *