Ibtila’i! Gobara ta tashi a Block D da E Line Yan Tumatur, kasuwar Sabon Gari Kano

1000050027

A yau ne da misalin karfe Sha daya da Arba’in da biyar 11:45 AM na ranar yau Laraba wuta ta kama wani gini dauke da bine hawa uku,a cikin kasuwar ta Sabon Gari.

Sai dai bayan an sanar da hukumar kasuwar,Nan take,JAMI’IN hulda da JAMA’A,Ado Haruna Muhd ya sanar da Yan kwana kwana na cikin kasuwa da kuma na jiha,inda Nan take bada jimawa ba aka kashe wannan wuta.

Haka kuma, shugaban hukumar Alhaji Abdul Bashir Hussien ya tabbatar da cewa babu asarar  dukaya ko daya da akayi,sakamakon shagunan kimanin guda Ashirin babu Dan haya ko daya aciki,saboda ginin kansa ba a kammalashi ba.

Abdul Bashir ya yabawa jami’ an tsaron cikin kasuwa da kuma hukumar Yan sanda na cikin kasuwa,inda D P O muhammad Abubakar da kansa ya a wannan wuri har sai da wutar ta mutu.

A bangan taren Yan kwana kwana na cikin kasuwa da kuma na Jiha   shugaban ya bayyana jin dadinsa kan yadda suka dukufa aiki batare da Bata lokaci ba,har sai da suka kauda wannan Gobara.

Daga karshe ya ce dalilin da haddasa wannan Gobara baikamata ace hakan na faruwa ba,ya kuma ce zasu dauki mataki akan wadanda suke hada wannan gobara,daga karshe ya ja hankalin Yan kasuwa kan duk sanda suka ga wani Abu Wanda Basu gamsu da shi ba,su gaggauta sanar da hukumar kasuwar domin daukar batakin gaggawa.

Ya godewa Allah (SWT)  Wanda cikin ikonsa ne aka kashe wannan wuta, da kuma gwamnatin Jihar Kano karkashin hazikin gwamna Engr, Abba Kabir Yusuf

Ado Haruna Muhd
Jamiin hulda da jamaa
Na kasuwar Sabon Gari singa da Galadima.

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *