Ibtila’i: An Yi Garkuwa Da Ma’aikatan Wucin Gadi Na INEC 17 Yayin Tafiya Aiki

Alfijr ta rawaito Hoodlums sun yi garkuwa da ma’aikatan wucin gadi 17 na Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) da aka tura zuwa unguwanni 19 a karamar Hukumar Ideato ta Kudu a Jihar Imo.

An yi garkuwa da su ne a kan hanyarsu ta zuwa aiki.

Sai dai an tattaro cewa ‘yan sandan sun yi gaggawar ceto su daga baya.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, mai magana da yawun hukumar ta INEC na jihar, Dokta Chineye Chijioke-Osuji ya ce “an ceto su ba tare da kayayyakin zabe da BVAS ba.”

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijr Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 

https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *