Hukuncin Da Kotun Ɗaukaka Ƙara Ta Zartas  Kan ADC da Wasu Jam’iyyu Huɗu

IMG 20260616 WA0737

Editor:

Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Abuja ta bayar da umarnin dakatar da aiwatar da hukuncin da Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke, wanda ya umarci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta soke rajistar jam’iyyun siyasa biyar.

A hukuncin da ta yanke ranar Talata, kwamitin alkalai uku na Kotun Ɗaukaka Ƙarar ya soki Mai Shari’a Peter Lifu na Babbar Kotun Tarayya bisa ci gaba da sauraron ƙarar da kuma yanke hukunci a kan lamarin.

Kwamitin ya bayyana cewa hakan ya faru ne duk da cewa tun da farko Kotun Ɗaukaka Ƙara ta bayar da wani umarni kan batun, kuma shari’ar tana gaban kotun domin sauraro.

Adon haka, Kotun Ɗaukaka Ƙarar ta ba da umarnin dakatar da aiwatar da hukuncin har sai an kammala sauraron ƙarar.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa Mai Shari’a Peter Lifu ya umarci a ranar Litinin da a soke rajistar jam’iyyun siyasa biyar.

Jam’iyyun da abin ya shafa sun haɗa da jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), Action People’s Party (APP), Action Alliance (AA), Zenith Labour Party (ZLP) da kuma Accord Party (AP).

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *