Hukumar kula da Manyan Asibitocin Jihar Kano ta magantu dangane da Ma’aikatan wucin-gadi da ta dakatar da aikinsu a Asibitocin gwamnati.
Alfijir Labarai ta rawaito hakan na kunshe ne cikin wata sanarwar da Samira Suleiman ta aika wa manema labarai a madadin shugaban hukumar Dakta Mansur Mudi Nagoda.
Sanarwar ta ce ma’aikatan wucin-gadin ba korar su aka yi ba kamar yadda wasu suke zargi, sai dai an dakatar da su ne don tantance su domin sanin tabbacin cika ka’idar aiki kafin daukar su da kuma sanin sahihancin adadinsu gami da yadda ake biyan su kudaden (allowance).
A baya an yi kuskuren daukar ma’aikatan wucin-gadin, lamarin da ya sa ake cirar wani kaso daga kudaden Inshorar Lafiya na ma’aikata, aka rika biyan su wanda hakan ya saba ka’ida, lamarin ya sa bayan binciken da Ma’aikatar Lafiya ta jihar Kano ta gudanar ta gano cewa a Asibitocin kwararru na Murtala Muhammad da na Sir Muhammadu Sanusi kawai akwai ma’aikatan wucin-gadin sama da Dari biyar (500). In Ji sanarwar
Ta kara da cewa “su dai ma’aikatan wucin-gadi ba takardar daukar aiki ce da su ta din-din-din (permanent and pensionable) ba, an dauke su ne saboda bukata ta wani lokaci, in kuma ana bukatar aikinsu sai a sabunta musu takardunsu.”
Sanarwar ta jero wadansu tambayoyi da suke da bukatar amsa, wadanda aka fitar kamar haka:
- Ina namu ma’aikatan wadanda suke a kan tsarin albashi na gwamnati?
- Daga ina asibitoci suke samun kudin da ake biyan ma’aikatan wucin-gadin (casual) sama da dubu daya da dari biyar?
- Ma’aikatan wucin-gadi su ba a dauke su aiki na din-din-din ba(permanent and pensionable) domin ba sa cikin kasafin kudi na jiha, balantana kudinsu yake zuwa kai tsaye. A murtala da Nassarawa kadai akwai sama da (casual 500), daga ina ake samun kudin biyansu?
- Ma’aikatar lafiya ta jihar Kano ta yi bincike kuma ta gano cewar daga kudin inshorar lafiya ake zaftara ake biyan su maimakon samar wa ma’aikata masu hakkin kudin magani kyakyawa da kuma samun kulawar da ta kamata.
- Shin ana bukatar su ko kuwa, ta yaya suka kai wannan adadi? Ta alfarma ne ko ta sanayya?
“A wannan gabar ne aka yanke shawarar gudanar da tantancewa ta musamman, a gano adadi da ake bukata na gaskiya kuma tabbatacce.”
“Shugabannin asibitoci sun yi kuskure wajen karkatar da makudan kudi wajen biyan yan wucin-gadi (casual).
Sannan kuma a ba wa gwabnati shawara ta bar su ko ta ba su aiki na din-din-din wato (permanent offer), ko a sa su acikin kasafin kudin shekara mai zuwa”.
“Tambaya ta karshe ita ce mene ne makomarka a matsayin ma’aikacin wucin-gadi (casual) shekara da shekaru ba (pension ba gratuity) ga bata lokaci?”
“Ya kamata mutane su gane cewa ba ma son mu cutar da kowa, amma dole mu gyara kwamachalar da ke faruwa a asibitocinmu in har muna so mu samu gyara mai inganci,” in ji Nagoda
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/K8z1chFesJeCf99QehWJPo