Takaitattun Labaran duniya na Yammacin Litinin 16/10/2023 01/04/1445AH

best seller i

Daga Baba Usman Gama

Najeriya ta tsara naira tiriliyan 26 a matsayin kasafin kuɗi na 2024

Kotun ɗaukaka ƙarar da ke zama a Abuja ta ce akwai ƙuri’un da ba halastattu ba cikin waɗanda aka kaɗa wa Mista Abbo na jam’iyyar APC, bisa la’akari da Dokar Zaɓe ta 2022.

Shugabar Kotun Ɗaukaka Ƙara a Najeriya, Mai Shari’a Monica Dongban-Mensem, ta ba da umarnin a mayar da duk Ƙararrakin da aka ɗaukaka na shari’o’in zaɓen watan Fabrairu da na Maris zuwa Abuja da Legas.

Zan iya sadaukar da rayuwa ta wajen magance ta’addanci a Katsina — Gwamna Radda

Ma’aikatan Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na KEDCO sun rufe ofishinsu saboda zargin ba a biyansu kudin fanshonsu na tsawon watanni 72 a kano

Gwamnatin Kano ta shirya kaddamar da tallafin kayan karatu ga makarantun gwamnati da ke Kananan Hukumoni 44 na jihar.

Tuɓaɓɓen Ɗan Daba mai suna “Chile Mai Doki” ya zama “Constabulary” a kano

Ban Ji Dadin Rashin Halartar Wasu ‘Yan Fim Wurin Taron Murnar ‘Sarauniyar Ado’ Da Aka Ba Ni Ba, Cewar Teema Makamashi

Yan Gudun Hijira A Yobe Suna Samun Kulawa Na Musamman A Karkashin Gwamnatin Mai Mala

Hauhawar farashin na watan Satumba da ya kai mataki na 26.72 cikin 100, ya ƙaru ne karo na 9 a jere daga matakin kashi 25.8 cikin 100 a watan Agusta, kamar yadda alƙaluma daga hukumar ƙididdiga ta Najeriya suka nuna.

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya ce ƙasarsa ta taimaka wajen dakile matsalar ƙarancin abinci a duniya tare da yarjejeniyar hatsi da ta ba da damar fitar da hatsin Ukraine zuwa kasuwannin duniya ta Tekun Bahar Aswad.

Tun bayan yarjejeniyar birnin Oslo ta shekarar 1993, gwamnatocin Isra’ila da suka biyo baya suke watsi da asalin batun da yarjejeniyar ta kunsa kamar da kasar Falasdinu mai cikakkiyar ‘yanci.

Sashen watsa labarai na Hezbollah ya saki wani bidiyo a ranar Litinin da ke nuna yadda ake harbin kyamarorin da suke wasu wurare biyar a iyakar Labanon da Isra’ila, ta hanyar amfani da bindigogin da ake iya harbawa daga waje mai nisa.

Yadda dubban mutane ne a kasar philippines suka gudanar da zanga-zangar lumana a gaban, domin nuna goyon baya ga Falasdinawa.

Attajirin Balaraben nan dan kasar Qatar, Sheikh Jassim bin Hamad Al Thani, ya janye tayin da ya gabatar a kokarin sayen Manchester United.

Ricardo Kaka a cikin 2021: “Ban damu ba idan yarana sun san cewa na taba zama dan wasa mafi kyau a duniya. Saboda nafison so su dauke ni a matsayin mafi kyawun uba a duniya”

Atletico Madrid ta sanar da Barcelona cewa a shirye take ta siyar da Joao Felix amma akan Yuro miliyan 80.

Barcelona anata bangaren, ta na shirin kara karbar aron Felix na tsawon kakar wasa me zuwa kuma ta saye shi na dindindin kan Yuro miliyan 40 a shekarar 2025, in ji Diario Sport.

Kungiyar Real Madrid ta aike da ‘Yan leken asiri don kallon Jobe Bellingham na Ingila, a wasan ‘yan kasa da shekaru 19 a lokacin hutun kasa da kasa, in ji Jaridar (El Nacional)

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/K8z1chFesJeCf99QehWJPo

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *