Alfijr
Alfijr ta rawaito hukumar kare hakkin mai saye da mai sayarwa ta Jihar Kano, watan KSCPC ta samu nasarar kama wani matashi mai suna Inuwa Muhammad mazaunin unguwar Kurmawa dake karamar hukumar birni a ranar Laraba 23/02 /2022.
Alfijr
Mukaddashin kakakin hukumar Umar Dan Kada ya bayyanawa yadda suka yi nasarar damke Inuwa wanda yake yin Sojan Gona da sunan cewa shi ma’aikacin hukumar ne.
Dan Kada ya kara da Cewar, sun samu rahoton yana yin amfani da wannan damar yana karbar kudade a wajen mutane musamman ‘yan kasuwa.
Alfijr
Saboda haka Hukumar tana Kira ga al’umma suyi hattara domin irrin wadanan bata garin, kuma suna nan zasu miki shi ga kuliya don girbar abinda ya shuka.