Daga AAminu Bala Madobi
Gwamnatin tarayya ta bukaci ‘yan Najeriya da su dauki keke a matsayin wata hanyar zirga-zirgar ababen hawa sakamakon kawar da tallafin man fetur da kuma tabarbarewar tattalin arziki.
Alfijir Labarai ta rawaito Musa Ibrahim, Daraktan kula da harkokin sufuri da zirga-zirgar ababen hawa na ma’aikatar sufuri ta tarayya ne ya bayyana haka yayin taron wayar da kan masu ruwa da tsaki a Abuja.
Ibrahim ya kara da cewa, sauya keken zai rage hadurran ababen hawa da kuma samar da tsaftataccen muhalli.
Ya kuma bayyana cewa hawan keke na iya zama wata hanya ta kawar da talauci da samar da lafiya da ci gaba mai dorewa.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb
Gaskiya wallahi janye tallafin Mai Babu abinda ya haifar face da mutane a halin takura da matsin rayuwa wani kudin suffirin da xai biya idan ya biya nawa yasamu nawa yakaiwa iyalansa nawa ya ajiye ko takwana amatsinmu na talakawa Allah ya mana suttura duniya da lahira
To munji amma bazamuyi ba seme
To munji mukoma anfani da Keke shi Wanda ya Fadi hakan yaje yasaiwa Mai Darrin hula tukuna mugaye in Allah ya yarda bazakuji dadin mulkin kuba