An Maka Maimartaba Sarkin Dutse A Gaban Kotun Musulunci

Matar majigayi Mai Martaba Sarkin Dutse, Hajiya Asiya Nuhu Sanusi ta maka mai martaba Sarkin Dutse, Ahaji Hamim Nuhu Sanusi zuwa kotun daukaka kara ta Shari’a kan hakkin gado.

Alfijir Labarai ta rawaito karar da lauyanta, Barista Abdulhali Ali Esq, ya gabatar matar tsohon Sarkin da wasu mutane bakwai suka shigar da Sarkin da wasu mutane shida a matsayin wadanda ake kara a gaban kotun shari’ar musulunci ta jihar ta 1, inda suke kalubalantar hukuncin da wata kotu ta yanke a baya.

Alkalin Kotun daukaka kara ta jihar, karkashin jagorancin Khadi Ado Birnin Kudu shine ake zarginsa da yin kuskure a shari’ar gadon da ‘yan uwan suka shigar a gabansa.

A cikin karar mai lamba SCAJG/CV/2023, uwargidan tsohon sarkin tana neman kotun daukaka kara da ta tantance ko karamar kotun ba ta yi kuskure ba a lokacin da ta yanke hukuncin cewa wata kadara mai lamba 17 JGNL/DU/RES /94/264, wanda marigayi mijinta ya ba ta lokacin yana raye wanda take neman kotun data sanya wannan dukiya a matsayin dukiyar iyali.

Ta kuma bukaci kotun daukaka kara ta tantance ko hujjojin da ta bayar a kotun na wata takarda da marigayi sarki ya sanya wa hannu mai lamba LPR/DU/3 da kuma mai lamba JGNL/DU/RES/94/511 wanda take ganin ya isa ya tabbatar da mallakinta ne.

Kotun ta bayyana cewa marigayi Sarkin kafin rasuwarsa ya baiwa kowacce daga cikin matansa gidaje biyu, amma Alkalin ya amince da karban kyaututtukan ga sauran matan tare da karbar nata tare da mayar da dukiyar a matsayin dukiyar iyali.

Ta bayyana maimartaba marigayi tsohon sarkin a matsayin jajirtaccen mutum kuma mutum na gari.

Maimartaba marigayi tsohon sarkin dutse Nuhu Muhammadu Sunusi ya rasu a ranar 30 ga watan janairun 2023. Kuma ya rasu yabar mata 2 da yaya 13 kuma ya rabu da wata matarsa kafin rasuwarsa.

Solacebase

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb

One Reply to “An Maka Maimartaba Sarkin Dutse A Gaban Kotun Musulunci”

  1. Salam. Ina bai wa mai martaba Sarki shawarar su karbi ikirarin matar mahaifinsu na cewa ya ba ta kaddarar nan. Haba ai kun fi karfin haka. Ban ji dadin labarin ba. Tun kan na karanta labarin na ce Sarki ya yi kuskure a nan da ya bar maganar ta je kotu. Da kuma na karanta labarin, sai na kara gaskata ra’ayina. Da dattaku aka san Sarki, ba da bin hakki ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *