Gwamnatin Najeriya Ta Kara Kudin “Passport” A Kasar

Screenshot 20240822 105700 Chrome

Gwamnatin tarayya ta sanar da karin kudaden karbar Passport din Najeriya daga ranar 1 ga Satumba

Alfijir labarai ta ruwaito hakan ya fito ne ta bakin mai magana da yawun hukumar shige da fice ta kasa (NIS), DCI Kenneth Udo, a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba.

A cewarsa, daidaita kudaden na daga cikin kokarin gwamnati na tabbatar da inganci da tsaron Passport din Najeriya.

Yanzu farashin “passport” da ake yi N35,000 mai shafuka 32 na tsawon shekaru 5 ya koma N50,000. Sai kuma “passport” mai shafuka 62 na shekaru 10, ya tashi N70,000, ya koma N100,000.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *