Gwamnatin Jihar Kano ta amince da ware kimanin naira biliyan 15.6 domin biyan hakkokin tsofaffin kansiloli da suka yi aiki tsakanin shekarar 2014 zuwa 2024, a lokacin gwamnatin tsohon Gwamna Abdullahi Umar Ganduje karkashin jam’iyyar APC.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na jihar, Comrade Ibrahim Abdullahi Waiya, ya fitar jim kaɗan bayan kammala zaman majalisar zartaswa karo na 27, wanda aka gudanar a gidan gwamnatin jihar dake unguwar Kwankwasiyya.
Sanarwar ta bayyana cewa jimillar adadin kuɗin da aka ware domin biyan waɗannan hakkoki ya kai ₦15,667,634,645.10.
Haka zalika, majalisar ta amince da kashe ₦5,386,380,955.00 domin daukar nauyin dalibai 1,002 da za a tura karatu zuwa kasashen waje a zagaye na biyu na shirin tallafin karatu, da kuma wasu makarantun cikin gida a Najeriya.
A wani bangare na taron, an kuma amince da ware ₦11,000,000.00 domin biyan alawus na watanni 11 ga ma’aikatan da ke aikin tsaro a gandun daji — musamman ma’aikatan Ma’aikatar Muhalli da Sauyin Yanayi guda 100.
Gwamnatin Kano ta ce wannan mataki na daya daga cikin tsare-tsaren inganta walwalar ma’aikata da ci gaban ilimi a fadin jihar.
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD