Gwamnatin Kano ta Sake Tura Rukunin Ɗalibai Kashi Na 4 Zuwa Kasar India

Abba Gida Gida

Rukuni na hudu, ɗauke da ɗalibai 150 da gwamnatin Kano mai ci ta dauki nauyin karatunsu a ƙasashen waje sun tashi zuwa ƙasar India domin yin karatun digiri na biyu a fanni daban-daban.

Alfijir Labarai ta rawaito cewa Tallafin karatun na daya daga cikin manya-manyan alkawura da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi lokacin yakin neman zaben sa, inda bayan ya hau mulki, ya dauki nauyin ƴan asalin jihar Kano su dubu 1,100 domin kai su ƙasashen waje su yi digiri na biyu.

Tuni dai aka fara shirin inda a yau Juma’a rukuni na huɗu ya tashi zuwa kasar India daga filin jirgin saman Malam Aminu Kano, da misalin ƙarfe 7:30 na safe.

Da yake sanyawa da manema labarai jim kadan bayan tashin ɗaliban, Kwamishinan Ilimi mai Zurfi na jihar, Dr Yusuf Kofarmata, ya ce za su sauka a Legas ne kafin su wuce zuwa India.

A cewar sa, da saukar su a India, za a kwashe su zuwa jami’o’i daban-daban da za su yi karatun su a fannonin ilimi daban-daban.

Ya kara da cewa Tallafin karatun na daya daga cikin manya-manyan alkawura da Gwamna Yusuf ya dauka kuma ya ke cika su tun ba wanda kujerar mulki a jihar.

Domin Kallon Shirin FATAKE Mai Dogon Zango Season 1 Da Kuma CIgaba Da Kallon Season 2, Danna wannan Link din👇

https://youtube.com/@ukentertainmentkano?si=PPtuxJz76OuNP_oI

Dr Kofarmata ya kuma yi nuni da cewa ɗaliban da iyayen su na cike da farin ciki da godiya ga Gwamna Yusuf bisa wannan tagomashi, inda ya yi kira gare su da su dage su yi karatu su kuma zama wakilan jihar da ma Nijeriya baki daya a ƙasashen da aka kai su.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *