Gwamnan Zamfara Ya Ɗauki Tsatstsauran Mataki Akan Tsaro A Jihar

Ya ƙara da cewa, jami’an tsaron da ke sintiri a waɗannan hanyoyi sun haɗa da sojojin ƙasa, sojojin sama da ‘yan sanda

Alfijir Labarai ta rawaito Gwamnan Jihar Zamfara ya ɗauki matakin zuba jami’an tsaro a manyan hanyoyin da ke fuskantar barazanar ‘yan bindiga.

Idan ba a manta ba, a zaman Majalisar Tsaro ta Jihar Zamfara wanda aka gudanar makon da ya gabata, Gwamna Dauda Lawal ya yi ƙorafi ga shugabannin ɓangarorin tsaro na jihar kan wasu hanyoyi da ‘yan bindiga ke cin karensu babu babbaka, musamman hanyar Gusau zuwa Funtua; Magami zuwa Dangulbi zuwa Dan Kurmi zuwa Anka, da kuma hanyar Magami zuwa Dansadau.

Mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, a wata sanarwar manema labarai da ya fitar yau Juma’a a Gusau, ya ce, zuba jami’an tsaro a hanyar Gusau zuwa Funtua da sauran hanyoyi na daga cikin shirin gwamnatin don tabbatar da kawo ƙarshen matsalar tsaro.

Ya ƙara da cewa, jami’an tsaron da ke sintiri a waɗannan hanyoyi sun haɗa da sojojin ƙasa, sojojin sama da ‘yan sanda.

Ya ce: “A taron Majalisar Tsaro ta Jihar Zamfara wanda aka yi makon da ya gabata, Gwamna Dauda Lawal ya nemi shugabannin sojoji da ‘yan sanda su tura motoci masu silken a CSK da APC domin yin sintiri a muhimman hanyoyin da ‘yan bindiga ke ta’asa.

“Haka kuma gwamnan ya yi wa shugabannin jami’an tsaron alƙawarin duk wani tallafi da suke buƙata don yiwuwar aikinsu ba tare da wata tangarɗa ba.

“Cikin matakan da gwamnatin Dauda Lawal ke ɗauka don magance wannan masifa ta rashin tsaro ne ya sa ta bayar da umurnin a rufe wasu kasuwanni da ake amfani da su wurin cinikayyar shanu da tumakin sata.”

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@musa_bestseller

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *