Gwamnan Kano ya nada Ahmad Musa shugaban ƙungiyar Kano Pillars

IMG 205735 04725 1751659071909

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya naɗa Ahmed Musa a matsayin sabon janar manajan ƙungiyar ƙwallon kafa ta Kano Pillars.

Sanarwar na kunshe ne ta bakin mai magana da yawun gwamnan Sanusi Bature Dawakinya bayyana a Yau ne Juma’a

Musa mai shekaru 32 shi ne kyaftin ɗin tawagar Super Eagles ta Nijeriya, duk da dai bai faye buga wa ƙungiyar wasanni ba a ‘yan shekarun nan.

Masu nazari kan harkokin ƙwallo a Nijeriya na ganin wannan sabon muƙami zai iya zama dadlilin da Ahmed Musa zai yi ritaya daga ƙwallon ƙafa.

Ɗan wasan dai ya taka rawa sosai a harkokin ƙwallo da cigaban matasa a ƙasar, kuma a yanzu yana buga wa ƙungiyar ta Kano Pillars wasa bayan dawowarsa Nijeriya

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *