KASIDAR EUROPEAN CHAMPIONS LEAGUE  (RUWAYA TA BIYU) Wallafar Professor Salisu Shehu

FB IMG 1751717995763

Da sunan Allah Shi Daya
Zan fara bayani bai daya.

Rabbu Kai Tilo ne Kai Daya
Ba kama a gareKa gaba daya.

Duk halittun kas da samaniya
Kai ne Ka yiwosu gaba daya.

Rabbana saita mini zuciya
Nai bayani ba wata zamiya

Nai salati na yo tahiya
GA Abin kaunarmu gaba daya.

Al–Bashiru Aminin duniya
Ka ji Mai cetonmu gaba daya.

Ni nufina zan yi matashiya
Ga shababu su bar sharholiya.

Watakila a yo mini tambaya,
Kan batun me zaka matashiya?

Kan batun kwallon Birtaniya,
Wofin banza na Pirimiya.

KO batun kwallo na Spaniya,
La Liga abin hauragiya.

Ko batun kwallon Almaniya,
Bundus Ligar sharholiya.

Wasu ma don sakarcin tsiya,
Da Faransa suke yin tutiya.

Masu zagin Khairul Anbiya,
Masu PSG Ibilishiya.

Ga Juventus can ta Italiya,
Wasu kanta suke ta hayaniya.

Masu sonta su ce mata gimbiya
Ba karatu sai dai tankiya

Wasu har Azumi fa suke niyya,
Don sadaukarwa ga Spaniya,

Ko su yo yankar qurbaniyya,
Zallar kaunar Barceloniya.

Hauma-hauma bidirin tsiya,
Wai ana kwallon Biritaniya.

Ko ka gansu suna ta karabkiya,
Wai ana kwallo da Valencia.

Ko ka gansu suna ta fagamniya, 
Wai ana kwallo da Burussia.

Ko ka gansu suna ta gaganiya,
Jamus wai ta ci Italiya.

Ko ka jisu suna ta hatsaniya,
Wai ana buga kwallon Duniya.

Ko su rinka yawan barababiya,
Wai su ne ‘yan Arseneliya.

Ni dai da na kalli pirimiya ,
Gara nai shukar tumfafiya.

Ko na samu kwadonmu na yadiya,
Nai ta ci don ta fice taliya.

David Beckham tuni ya riya,
Baya son Ummah Islamiyya,

Haka ma Chelsean Birtaniya,
Basu son jinsin Ifrikiyya.

Yau ina King Pele a Duniya?
Balle Maradona mazan GIYA!

Zico 9 ba ma jin duriya,
Roger Miller a nan Ifriqiya.

Wai ina Zinadine ne Duniya?
Na Faransa tsatson Algeria?

Shin ina Kanun Naijeriya?
Su Taribo, Okocha a Duniya?

Duk suna nan raye a Duniya,
Amma sam ba wata duriya.

Yau su Neyma suke buga Duniya,
Ronaldo da Messi suna buga tankiya.

Kan gwanintar kwallon Duniya,
Can ta matse musu sakarcin tsiya .

Ga su Manchester Britaniya,
Team ne biyu  ‘yan gabar tsiya.

Masu sonsu a nan Naijeriya,
Basu son juna gabar tsiya.

In suna musun Manchestiya
Ka ga mamakin hauragiya

Huruwar hanci da ta jijiya,
Ga bankaura da hayaniya.

In ka jisu suna buga tankiya,
To a nan kusa ka ji ashariya.

Sun mance nasihar gaskiya,
Sunnar Manzo Bahanifyya.

Duk Musulmi kab baki daya,
Yan uwan juna ne bai daya.

Mun gani shiriyar Bahanifiya,
Millarmu ta Khairul Anbiya,

Wanda duk fa ka soshi a Duniya,
Tare dai kuke Ranar Ghashiya.

Yan shababu ku tambayi zuciya,
Wa kuke kauna nan Duniya?

Shin Sahabban Khairul Anbiya?
Ko manyan kwallon Duniya?

Masu yin shagalin sharholiya?
Masu kwana zuzzukar giya?

Sui ta tambelen hauragiya,
Da rawa da kidar garalgajigalliya.

Ya shababu ku zo duka bai daya
Ga nasiha kukan kurciya

Kui riko da tafarkin gaskiya
Garkuwa kenan ga hayaniya.

Duk samarin wannan nahiya,
Mui ta himma ba hauragiya.

Na tino gargadi na mazan jiya,
Zungur su Sa’adu abin biya,

“Mu dai ilimi muka tambaya,
Ko a London ko a Arebiya”.

Ya shababu ku lura da Duniya
Mai bugarwa ce tamfar GIYA.

Lokacin da mutum ya ji lafiya,
Baya komai sai barnar tsiya.

Balle kuma in ya ga dukiya,
Ta taru irin zinariya,

Sai ka ganshi yana ta fahariya
Ga hululu da yin sharholiya.

Sai ya rinka zuwa Birtaniya,
Old Trafford can a Stadiya,

Wani ko ya nufanci Italiya,
Inter Milan yan hauragiya,

Ko ya zoshi ya kirkiri kungiya,
Shi yake yanke mata cibiya,

Yai ta kan renonta da DUKIYA,
Har ta kai wata yar hamshakiya,

Maimakon ya yi Zakkar dukiya,
Ko ya yo sadaka mai jariyah,

Amma sai dai ya yi tutiya,
Wai yana da zaratan kungiya.

Ya Allah Kai mana kariya
Daga bin shahawowin zuciya

Kar mu fada rudun duniya,
Mui ta bankaura da hayaniya.

Tabbatar mana tsarkin zuciya,
Mui ta addini bisa gaskiya.

Tabbatarmu a kan Bahanifiya,.
Sunnarmu ta Khairul Azkiya.

Nai salati na yo tahiya,
Ga Aminu Rasulun Gaskiya.

Mustafa Mai ceton gaskiya,
Shi ne kuma Khairul Asfiya.

Nai yabo kuma na yi ta godiya,
GA Alimu Ilahun Gaskiya.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *