Alfijr
Alfijr ta rawaito, Hukumar EFCC reshen Kano a yau 17 ga Fabrairu, 2022, ta gurfanar da wani Auwal Sidi Sherrif a gaban mai shari’a Maryam Sabo ta babbar kotun jihar Kano.
Alfijr
Laifukan da ake zanginsa da laifuka ne biyar da suka hada da takardun jabu da karbar kudi ta hanyar karya.
Wanda ake zargin ya yi amfani da takardan jabu wajen siyar da fili mai lamba 352 TP/KAS/236A da ke Eastern Bye-Pass, Yan Awaki Unguwa Uku, karamar hukumar Tarauni, Kano.
Alfijr
Wanda ake zargin ya ce ya saya a hannun wani Alhaji Garba Abdullahi a shekarar 2014. , akan Naira 1,800,000.