Kotu Ta Daure Wani Tsoho Mai Shekaru 82 Da Wani Matashi Kan Laifin Tabar Wiwi

IMG 20180605 130113 099

Kotun majistray me lamba 90 dake zaman ta a madobi karkashin Jagorancin maishari’a Haj. NADIYA ADO SALE ta ɗaure wasu mutane guda biyu inda ake tuhumar su da laifin hadin kai da ta’ammali da tabar wiwi wanda ya haɗa da Ilyasu Idris mai shakaru 82, da Yakubu Ɗalha 35.

Alfijir labarai ta rawaito bayan karanta masu kunshin tuhumar su ne, suka amsa. nan take, nan kotu ta karanto musu hukunci Inda ta daure malam ilyasu Idris mai shekaru 82, tsahon makwanni uku babu zaɓin tara, akan laifin hada kai wanda mai sharia ta duba tsufan sa da kuma rokon da ƴaƴansa da kuma shi kansa yayi a gabanta na neman afuwa da sassauci, sannan kuma akan tuhumar samun su da tabar wiwi kimanin ɗauri 95 ta kuma daure shi wata shida ko zabin tara ta 50,000.

Mai Shari’a Nadiya ta kuma aike da abokin hulɗar tasa Yakubu Dalha gidan gyaran hali na tsahon shekara ɗaya babu zaɓin tara, akan laifin hada kai kuma an daure shi wata 6 ko zabin tarar dubu hamsin.

Mai shari’ar ta hana zaɓin tarar ne kasancewar Wannan ba shine karo na farko da jami’an tsaro ke gurfanar dasu don girbar abunda suka shuka ba.

Daga karshe Mai sharia tayi musu gargadi na zu zama mutanan kirki kuma su dauki Alkawarin daina saida kayan maye a wannan yanki na madobi jahar kano baki daya.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *