Dubun Wasu ‘Yan Fashi Da Makami Da Cika A Unguwar Ja’in Kano

Alfijr

Alfijr ta rawaito rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta samu nasarar cafke wasu mutane biyu da ake zargin ‘yan fashi da makami ne bayan sun kai hari tare da daba makami ga, wani mazaunin unguwar Ja’in Kade kano.

Mujahid Aminu mai shekaru 18 shine daya daga cikin wanda ake zargin, an kama shi ne bayan da wasu tarin jama’a suka samu nasara damke shi bayan da suka kaiwa mazauna unguwar hari, daga bisani ‘yan sanda suka kama dayan mai suna Sani Alkasim mai shekaru 18, shima a unguwar.

Da yake tattauna da manema labarai SP Abdullahi Haruna Kiyawa mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Kano ya ce, mun samu rahoton wasu ‘yan fashi da makami sun far wa wani mazaunin unguwar Ja’in dake Kano, inda suka daba masa wuka a kirjin sa, sannan suka tafi da wayarsa Infinix S5 da kudinsa ya kai Naira 98,000.

Alfijr

Kiyawa ya kara da cewa, an garzaya da wanda ya samu raunin zuwa asibitin kwararru na Murtala Mohammed Kano, inda aka kwantar da shi.

Da suke amsa laifinsu, wadanda ake zargin sun ce: “Mun same shi a gidansa yana sanya katin waya , muka karbi wayar muka tafi, sannan muka dawo muka daba masa wuka a kirjinsa, nan take ya fara ihu kuma an kama daya daga cikin mu.

Alfijr

Bayan kafirin suka da daya daga cikin ƴan fashin ya sha, an garzaya da shi asibitin kwararru na Muhammad Abdullahi Wase Kano inda aka duba shi daga nan aka maida shi hannun jami’an ‘yan sanda. Inji kiyawa

Da yake karin bayani, ya ce binciken da aka gudanar an sami nasarar kama wani Murtala Sa’idu Sharif mai shekaru 34 a Unguwar Ja’in dake Kano, wanda yake kerawa tare da samar da makamai ga ‘yan fashi da makami.

Alfijr