Rundunar Amotekun ta jihar Osun ta kama wasu mutane da suka kware wajen tono gawarwaki tare da cire sassan jikinsu domin yin tsafi.
A wata sanarwa a ranar Talata, 12 ga watan Disamba, mai magana da yawun Amotekun na jihar Osun, Adeniyi Adeshola Brown ya ce mutanen ukun sune; Kamilu Kehinde mai shekaru 43 mai sana’ar kanikanci da Akeem Hamzat direba mai shekaru 56 da kuma Wakeel Baka mai sana’ar tsibbu.
Brown ya bayyana cewa an kama su ne biyo bayan bayanan sirri da jami’an rundunar Iwo suka samu.
Ya ce: “A yayin da ake yi musu tambayoyi, wadanda ake zargin sun yi ikirarin cewa suna cikin harkar tono gawarwaki daga kaburbura; wanda sai su sayar wa masu saye da suke bukatarsu domin yin tsafin neman kudi”.
kakakin ya bayyana cewa kwamandan rundunar ta jihar Osun, Bashir Abiodun Adewinmbi, ya bayar da umarnin a mika wadanda ake zargin zuwa rundunar ‘yan sandan Najeriya domin gudanar da bincike na gaskiya da kuma gurfanar da su gaban kuliya.
Jaridar Isyaku
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp