Wata Sabuwa! Da Yiyuwar Jami’oi Su Sake Shiga Yajin Aiki A Najeriya

Da yuyuwar a sake fuskantar tafiya yajin aikin jami’oi a kasar nan a shekara mai zuwa, sakamakon kason da aka ware masu cikin kunshin kasafin kudin shekara mai zuwa bai taka kara ya karya ba, kamar yadda kungiyar malaman jami’oi ta kasa ta baiyana.

Alfijir labarai ta rawaito a hirarsa da manema labarai a ranar litinin, Shugaban kungiyar na kasa, farfesa Emmanuel Oshodoke, Ya  ce  a yayin yakin neman zaben shugaban kasa Bola  Tinubu, ya yi alkawarin karawa kasafin fannin ilimi kimanin kaso 15 cikin 100.

Sai dai kuma y ace  kungiyar  ta baiyana mamakinta kan yadda aka warewa bangaren ilimi naira tiriliyan 2 da bilyan 18, wanda ya kama kaso 7 da digo 9 cikin 100  na kasafin kudin,  kuma hakan ya saba ta tanadin hukumar bunkasa ilimi da raya al’adu ta majalisar dinkin duniya UNESCO, wadda ta bukaci a rika warewa bangaren kaso  26 cikin 100.

Dagan an shugaban kungiyar malaman jami’oin ta kasa  ya shawarci gwamnati da  ta yi zama na musamman da  ‘yan majalisar zartawa domin karawa  fannin ilimi kaso mai  tsoka a cikin kasafin kudi.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *