Daga Baba Usman Gama
Shugaba Tinubu ya buƙaci majalisar dattawa ta amince da naɗin sabbin kwamishinonin hukumar kidaya ta ƙasa (NPC).
Iyalan wadanda suka rasu sun maka gwamnatin Najeriya da rundunar Sojoji a Kotu, suna bukatar a biya su diyyar naira biliyan 33.
Majalisar Dattawa ta nuna ɓacin rai kan ƙarancin kuɗaɗen da aka ware wa Ma’aikatar Yaɗa Labarai a Kasafin 2024.
Jiragen sojin Najeriya sun kashe dan bindiga Ali Alhaji Alheri, wanda ya jagoranci sace dalibai mata na Jami’ar Tarayya ta Gusau da kuma yaran Dogo Gide.
Peter Obi, ya ziyarci mutanen da harin bam ya shafa a asibitin koyarwa na Barau Dikko da ke Kaduna ranar Talata.
Najeriya za ta tura kuraman jirage kan iyakokinta domin tabbatar da tsaro.
Bode George ya fadawa kusoshin da ke PDP su ajiye maganar sake dauko ‘dan takaran shugaban kasa daga yankin Arewa.
Wasu jaruman Kannywood sun roki Shugaba Tinubu da ya tabbatar da an yi adalci a shari’ar zaben gwamnan Jihar Kano da ke tafe a kotun koli.
‘Yan bindiga sun yi garkuwa da mutum a unguwar Dei-Dei da ke Karamar Hukumar Bwari a babban birnin tarayya, Abuja.
’Yan sanda sun kashe ’yan bindiga da ke yunkurin tare hanya su sace mutane a kan hayan Dutsin-Ma zuwa Kankara a Jihar Katsina.
NLC ta sa zare da gwamnati kan kin biyan ma’aikata N35,000 na Cire tallafi.
Gwamna Sani ya daura damarar dakile matsalar tsananin yunwa a yara kanana da rage mace-macen mata a Kaduna.
Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta samu nasarar cafke wasu shahararrun barayin mota da suka addabi jihar da makwaftan ta.
Libya ta mayar da wasu ‘yan ci rani na Najeriya da Masar kasashensu.
An gano gawawwakin ‘yan Isra’ila biyu da aka yi garkuwa da su.
Kotu a Japan ta yanke wa sojoji maza hukunci kan cin zarafin sojoji mata ta hanyar lalata.
An kashe aƙalla fararen hula 30 a wani hari da aka kai a kauyen Burkina Faso.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp