Dan Kasuwa Ya Nemi Kashe Matarsa Don Ya Kara Jari A Shagonsa

IMG 20231210 095643

Wanda ake zargi da yunkurin kashe matarsa saboda sayar da talabijin a Jihar Bauchi

Alfijir labarai ta rawaito an cafke wani dan kasuwa kan yunkurin kashe matarsa don ya samu damar sayar da talabijin dinsu ya kara jari a shagonsa a Jihar Bauchi.

Magidancin mai shekaru 35 ya shiga hannu ne bayan ya yi amfani da tabarya wajen dukan matar  tasa da nufin kashe.

Rundunar ’yan sandan Jihar Bauchi ta ce, magidancin, ya shaida wa masu bincike “cewa ya yi niyyar kashe matarsa ne don ya dauki talbijin dinsu ya sayar, ya samu kudi ya kara kaya a shagonsa.”

Kakakin rundunar, Mohammed Ahmed Wakil, ya ce an kai matar Asibitin Kwararru da ke Bauchi domin kulawar da ita a sakamakon munanan raunukan da mijin ya yi mata da tabarya

Bincike na farko ya nuna wanda ake zargin ya amsa tuhumar da ake masa ba tare da wata turjiya ba.

“Ya yi ikirarin cewar ya yi karyar cewa ’yan fashi sun shiga gidansu, shi ne ya shiga dakin da suke kwance da matarsa ​​ya ce mata ta rufe kanta da gyale.

“Sai ya fita ya je ya rufe fuskarsa da mayafi, sannan ya dauko tabarya ya dawo dakin ya fara dukanta da ita,” in ji kakajin rundunar.

Ya ce abin ya faru ne a ranar Asabar, 2 ga watan Disamba, 2023, kuma kwamishinan ’yan sandan ijhar, Auwal Mohammed, ya bayar da umarnin mika wanda ake zargin ga sashen binciken manyan laifuka don zurfafa bincike da kuma gurfanarwa a kotu da zaran an kammala bincike.

Aminiya

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *