Daga Baba Usman Gama
An kama ƴan sandan da suka roƙi baturiya kuɗi a jihar Oyo.
Gwamnan Katsina ya ba da umarnin dakatar da shugaban makarantar sikandire garin Dandume kan zargin neman ɗaliba.
Gwamnan Akwa Ibom ya rantsar da sabbin kantomomi 31 bayan amincewar majalisa.
Abdulmumin Jibrin ya ce karya ne NNPP bata tattaunawa da kowa a yanzu don hadewa Shugaban kasa Bola Tinubu kai.
Jam’iyyar SDP ta karyata batun yin maja da PDP da sauransu don kayar da Shugaban kasa Bola Tinubu.
Abdulrahman Sulaiman Kawu Sumaila yace saboda 2027 APC ke neman kujerar Abba Kabir Yusuf na Kano.
Wasu daga cikin mutanen da suka tsallake rijiya da baya a kauyen Tudun Biri sun bayyana yadda Allah Ya kubutar da su daga harin jirgin sama marar matuki da ya yi sanadiyar rasuwar sama da mutum 90.
Kamfanin Shell zai zuba jarin dala biliyan 5 domin samar da gas a Najeriya.
Gwamnati ta fara horas da ma’aikatan lafiya hanyoyin dakile yaduwar cutar diphtheria.
Likitoci sun ce wasu a cikin dakarun sojin Isra’ila da ke faɗa a mamaye ta ƙasa a Gaza, suna fama da wani matsanancin ciwon ciki sanadin wata cuta da ake kira “shigella”.
‘Yan sanda sun yi wa tsohon shugaban ƙasar Saliyo Koroma tambayoyi.
Sojojin wanzar da zaman lafiya a Kongo na ci gaba da ficewa daga ƙasar.
Dakarun majalisar dinkin Duniya sun kammala ficewa daga Mopti dake kasar Mali.
Seria A: Juventus ta sami nasara akan Napoli da ci 1:0 a wasan jiya.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp