Alfijr
Alfijr ta rawaito kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta dauki kocin Ajax, Erik ten Hag a matsayin sabon kocinta.
Erik ten Hag ya rabbata hannu har zuwa karshen kakar wasanni ta 2025 tare da damar karin wata shekara guda a kan kwantaragin nasa idan da bukatar hakan.
Man United ta biya Ajax Fam miliyan biyu a matsayin kudin sanya hannun kocin.
Alfijr
Kungiyar ta dauki tsawon lokaci tana tattaunawa da kocin kan yiwuwar sanya mata hannu, don ceto ta daga halin da ta shiga na samun koma baya da take
Manchester United ta bai wa Ten Hag cikakken ikon gudanarwar kungiyar da kuma sayen ’yan wasan da yake so a duk inda suke babu katsalandan