Cikakken Bayanin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu Kan Koken Al’ummar Kasa

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya fito gaba gaɗi domin share kukan al’ummar ƙasa musamman dan gane da halin matsi da ake ciki.

Alfijir Labarai ta rawaito Tinubu a jawabin da ya gabatar ta kafafen yaɗa labarai a yammacin yau, ya bayyana yadda gwamnati ta shirya antayo maƙudan kuɗaɗe ta fannoni da dama domin ragewa mutane raɗaɗin gyaran karayar tallafin mai da ake ciki a halin yanzu.

Ga kaɗan daga cikin tanade-tanaden:

  1. Bawa manyan masu masana’antu 75 jari mai rangwame har na naira biliyan ɗaya kowannen su. Wanda za su biya a tsahon watanni 60.
  2. Masu matsaƙaita da ƙananan sana’o’i za su amfana da naira biliyan 125 domin haɓɓaka jarinsu.
  3. Daga cikin waccan biliyan 125 gwamnati za ta bada ja’iri kyauta (mai haɗe da ƙa’ida) na naira 50,000 ga masu ƙananan sana’o’i mutum 1,300 a kowace ƙaramar hukuma.
  4. Sauran biliyan 75 za su tafi wajen masu matsaƙaitan sana’o’i inda za a bawa mutum 100,000 rance mai rangwame na naira 500,000 zuwa miliyan ɗaya wanda za su biya a hankali cikin shakara uku.
  5. Tunda sai da ruwan ciki ake janyo na rijiya, Shugaban Ƙasa ya bada umarnin fito da abinci har ton 200,000 tare da takin zamani ton 225,000 domin rabawa ga mabuƙata.
  6. Nan ba da jimawa ba gwamnati za ta samar da ƙananan moticin bus masu amfani da gas har guda 3,000 domin kawo rangwame a kuɗin sufuri da jama’a ke fama da shi. Waɗannan motoci za a raba su ne ga kamfanonin sufuri domin gudanar da su.
  7. Haka nan kuma gwamnati ta ware maƙudan kuɗaɗe domin noma hekta 500,000 a ɓanagarori daban-daban na ƙasar nan. Baya ga samar da abinci wannan shiri zai samarwa da matasa marasa aikin yi sana’a ta wucin-gadi.

A ƙarshe, ga waɗanda suka saurari cikakaken jawabin za su ji yadda Shugaba Tinubu ya nuna tausayawa da halin da ake ciki, ya bada haƙuri, ya kuma sha alwashin ƙawo ƙarshen wannan yanayi cikin gaggawa da taimakon Allah.

Wadannan na daga cikin manyan manufofin da shugaban ya zayyana a yau Litinin.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb

11 Replies to “Cikakken Bayanin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu Kan Koken Al’ummar Kasa

  1. a gaskiya sai mukara daggewa da alduoi gamida yadda shogaban kasa yayiwa yan mutalakawa bayanin gassaushe allah yasa muddace duniya da lahera daga naku zubairu yusuf fagge england nagode

  2. Slm alaikum. To Jama’a kuna de ganin abund ke faruwa kuma duk Wanda y bibiyi wannan bayani d idon basira yasan zance ne kawai kuma koda an iya gudanarda wadannan abubuwa bazasu magance komai b game d wahala d muke fama d ita. Za kuma kuce nagayamuku, Ni a ra’ayina bangoyi bayan wannan badakalar b mgn t gaskia, ai Gomnatin baya t gwadayin irin wadannan abubuwan d tayi ansami canjin d ake bukata? Amsar shine a’a. Sbd hka mu jama’a yakamata musan abunyi wa’yan nan b taimakonmu zasuyi ba.

  3. Allah yatabbatar da alkairin wannan kuduri da nai girma shugaban kasa ya tanada akan talakan najeriya

  4. Masha Allah, Allah yay riqo da hannayen shugabannimu, yasa duk abinda zasuyi ya zama na cigaban Al’uma ne.

  5. Mu gani a kasa Kamar yada aka janye subsidy ba tare da tacce-nacce ba, haka ma Abadan wannan tallafi ba tare da yimuna alkawalin island ba

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *