Hatsari Ya Rutsa Da Tawagar Gwamna ‘Yan Majalisu Sun Jikkata

Alfijr ta rawaito ayarin motocin Gwamna Samuel Ortom na Jihar Benue ta yi hatsari a kusa da garin Utokon da ke karamar hukumar Ado na jihar a yau Juma a.

Rahotanni sun ce Ortom da tawagarsa na kan hanyar su ta zuwa yakin neman zabe dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a Igumale helkwatar karamar hukumar Ado.

Rahotanni sun ce motar ta kubuce wa direban motan da ke cike da dandazon magoya bayan PDP ya bugawa wata mota kirar Jeep, da motar jami’an tsaro da wata bas cikin tawagar gwamnan.

Motocin da ke cikin tawagar sun hada da na mataimakin gwamnan jihar, Injiya Benson Abounu, Sanata Abba Moro, Mambobin majalisar wakilai na tarayya da yan majalisar dokokin jihar Benue, da wasu manyan jami’an gwamnati da jam’iyyar PDP a jihar.

Bayan faruwar lamarin cikin gaggawa motocin asibiti na gwamnatin jihar suka isa wurin da abin ya faru ta kwashe wadanda abin ya shafa ta tafi da su asibiti don yi musu magani.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/Cy5n7eXK4wrHMIEYBSYpcQ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *