ASUU Tayi Fatali Da Nadin Gawuna Da Wasu A Matsayin Shugabannin gudanarwar Jami’o’i

IMG 20240623 WA0013

Daga Aminu Bala Madobi

Kungiyar malaman jami’o’in Najeriya ASUU reshen jami’ar Bayero Dake Kano, ta yi watsi da nadin da aka yiwa Dakta Nasiru Gawuna a matsayin shugaban majalisar gudanarwar jami’ar.

Alfijir labarai ta ruwaito shugaban kungiyar ta ASUU Farfesa Ibrahim Tajo Suraj shine ya bayyana hakan. Yana Mai cewa tsarin da ya kai ga nada ‘yan siyasa a majalisun gudanarwar manyan makarantun ilimi na kasa ya saba wa dokokin da aka samar domin irin wannan nadin.

Idan za a iya tunawa, a satin da ya gabata ne, Gwamnatin tarayya ce ta nada Dr Nasir Gawuna da sauran fitattun mutane domin jagorantar kwamitocin koli a wasu jamio’i, isai dai zuwa yanzu lamarin na neman canza salo, na barin-baya-da-kura.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *