Arewa Oil & Gas Ta Ƙaddamar Da Sabon Shugaban AROGMA Yayin Babban Taronsu A Kano

A yau, mun samu wani ƙarin gagarumin ci gaba a tarihin fannin makamashi,”

Alfijir Labarai ta rawaito Ƙungiyar dillalan man fetur da iskar gas ta Arewacin Najeriya AROGMA ta kafa babban tarihi na gudanar da gagarumin bikin ƙaddamar da sabbin shugabanninta tare da kaddamar da ayyukanta a hukumance a wani gagarumin biki da ta gudanar a Kano.

Manyan mutane da mambobi da ɗimbin ƴan kishin ƙasa daga sassan Najeriya daban-daban ne suka yi dandazo domin halartar taron mai cike da tarihi, wanda ya kai ga ƙaddamar da sabon shugaban ƙungiyar wanda zai jagoranci muhimman al’amuran dillalan mai da iskar gas ɗin a wannan yankin.

Bashir Danmalam, wanda fitaccen jigo ne a masana’antar, ya zama shugaban ƙungiyar AROGMA mai albarka, a yayin wannan gagarumin taron.

An ba shi takardar shedar jagoranci, bayan da ya samu ƙwarewa ta lokaci mai tsawo a wannan fanni.

Bikin dai, ya samu halartar jama’a daban-daban, wadanda suka wakilci ɓangarori da sassa da dama na rayuwa da kuma yankuna daban-daban na Najeriya.

Waɗanda suka halarci taron sun fito ne daga sassa daban-daban na kasar, inda suka nuna irin tasirin da kungiyar ke da shi da kuma dacewa.

Taron ya kuma kasance wani dandali na ƙwararrun masana’antu, ‘yan kasuwa, da masu ruwa da tsaki dai suka haɗu domin nuna farin ciki da ci gaba da bunkasar harkar mai da iskar gas a yankin Arewa.

Bashir Danmalam ya ce, “A yau, mun samu wani ƙarin gagarumin ci gaba a tarihin fannin makamashi,” in ji Bashir Danmalam yayin jawabin karbar shaidar shugabancin.

“Kafa ƙungiyar AROGMA shaida ce ta haɗin gwiwar da muke da ita ta ciyar da muradun masana’antar mai da iskar gas a yankin Arewa, tare da sadaukar da kai ba tare da ƙaƙƙautawa ba, za mu samar da kirkire-kirkire, da samar da hadin kai, da inganta ayyuka masu ɗorewa waɗanda za su ciyar da wannan shiyya tamu gaba matuƙa.

“Ƙaddamar da wannan ƙungiya ta dillalan man fetur da iskar gas ta Arewa a Kano na nuni da cewa an sake mayar da hankali wajen yin amfani da dimbin albarkatun makamashi da albarkatun da yankin ke da shi, a cewarsa.

Yayin da sabon shugaban ya hau kan karagar mulki, ana sa ran ƙungiyar za ta iya sauƙaƙa huldar abokantaka, da inganta ƙa’idojin masana’antu, da bayar da gudummawa ga ci gaban tattalin arzikin yankin.

Bikin dai ya ƙunshi al’ada da zamani, wanda ya dauki hankulan al’adun gargajiyar Arewa tare da rungumar yanayin da fannin makamashi ke da shi.

Taron dai ya nuna ba wai sabon zamani ne na AROGMA kadai ke da shi ba, har ma da himma wajen tsara makomar harkar mai da iskar gas a yankin arewacin Najeriya.

Haka kuma a yayin da mahalarta taron suka tashi daga wajen bukin cikin farin ciki da annashuwa, ya bayyana a fili cewa Arewa Oil and Gas ta ƙuduri shirya wani muhimmin horo da zai mamaye duk fadin masana’antar, wanda hakan ya zama babban jigo a ci gaban tattalin arzikin yankin.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/Jmw5CBsPV6H3DbSgnlFUHM

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *