Daga Aminu Bala Madobi
“Ina addu’a ga kokarin da kasashen duniya ke yi na samar da mafita domin amfanin kowa.”
Alfijir Labarai ta rawaito Paparoma Francis na fadar Vatican ya yi kira da a samar da zaman lafiya yayin da kungiyar ECOWAS a karkashin shugaba Bola Tinubu ta yi watsi da shirin mika mulki ga gwamnatin Nijar na shekaru uku.
A ranar Lahadin da ta gabata, kwamishinan harkokin siyasa, zaman lafiya da tsaro na ECOWAS, Abdel-Fatau Musah a wata hira da BBC ya bayyana cewa ECOWAS ba za ta amince da shirin mika mulki da gwamnatin mulkin soja karkashin jagorancin Abdourahmane Tchiani ta gabatar a Jamhuriyar Nijar ba.
Tchiani a karshen mako, ya ce zai yi murabus a cikin shekaru uku kuma ya yi gargadin cewa duk wani shiga tsakani da sojojin kasashen waje za su yi, abune da zai zo ba mai dadi ba.
Ya bayyana hakane a wani jawabi da aka watsa ta gidan talabijin ta Tele Sahel, “Burin mu ba shine mu kwace mulki ba. Lokacin canji ba zai wuce shekaru uku ba; a halin da ake ciki, an bukaci jam’iyyun siyasa da su mika ra’ayinsu na mika mulki cikin kwanaki 30.
Gargadin nasa ya biyo bayan isowar tawagar ECOWAS a kasar domin tattaunawa kafin ta yanke shawarar shiga tsakani na soji a kan mulkin soja.
Sai dai a cikin hirar Musah ya ce dole ne a mika mulki cikin kankanin lokaci.
Ya ce “Ecowas ba ta sake amincewa da wani tsawaita lokacin mika mulki a yankin na. Dole ne kawai su shirya don mikawa farar hula mulki cikin kankantar lokaci.
A ranar Asabar din da ta gabata ne tsohon shugaban mulkin soji, Janar Abdulsalami Abubakar (rtd), ya jagoranci tawagar kungiyar ECOWAS zuwa Nijar a wani yunkuri na karshe na diflomasiyya na cimma sulhu da gwamnatin mulkin Nijar.
Tawagar ta gana da firaminista Ali Zeine wanda ya tarbe su a filin tashi da saukar jiragen sama ya kuma kai su fadar shugaban kasa.
Daga baya sun gana da hambararren shugaban Nijar Mohamed Bazoum, bayan sun gana da shugaban mulkin soja Janar Abdourahamane Tchiani.
A halin da ake ciki, Shugaban mabiya darikar katolika na duniya ya yi kira da a samar da zaman lafiya a jamhuriyar Nijar tare da yin kira ga dukkan bangarorin da abin ya shafa da su dauki matakin da ya dace.
Da yake jawabi a dandalin St. Peter’s Square, ya ce: “Ina addu’a ga kokarin da kasashen duniya ke yi na samar da mafita domin amfanin kowa.”
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/Jmw5CBsPV6H3DbSgnlFUHM