Masu Ɗaukar Hoto Na Arewa Sun Magantu Kan Hannatu Ministan Fasaha Da Al’adu

Kungiyar masu daukar hoto ta Arewa da kwararrun masu daukar hoto na Najeriya reshen Kano sun taya sabuwar ministar fasaha, al’adu da tattalin arziki, Hannatu Musawa murnar nadin da shugaba Tinubu ya yi mata

Alfijir Labarai ta rawaito a wajen taron bikin ranar daukar hoto ta duniya da aka gudanar a Kano ranar Asabar, kungiyoyin biyu sun kuma yi alkawarin bayar da goyon bayansu ga Musawa, wanda Tinubu ya rantsar a ranar litinin.

Da yake nasa jawabin shahararren mai daukar hoto a Arewacin Najeriya, Sani Maikatanga, ya ce a shirye suke su marawa Hannatu baya domin samun nasara a sabuwar ma’aikatar.

A cewarsa, nadin Musawa ya dace kuma ya cancanta, inda ya kara da cewa shugaba Tinubu ya sanya kwarya a gurbin ta.

Musawa tana da kwarewar da ake bukata don ciyar da sabuwar ma’aikatar gaba, don haka muna fatan cewa da ita a ma’aikatar za su bunkasa sana’ar daukar hoto, bidiyo da fina-finai zuwa ga duniya.

Maikatanga ya shafe sama da shekaru 30 a sana ar daukar hoto, ya bayyana farin cikinsa kan yadda taron ya samu damar hada kan masu daukar hoto na Kano, da kulla alaka da zumunci.

Ya kuma kara karfafa gwiwar matasa da su mai da hankali kan daukar hoto, maimakon gararamba a gari.

Shima a tattaunawar da Alfijir Labarai ta yi dashi (DR) Bala Abdullahi wanda aka fi shini da (Balancy) kuma shugaban kamfanin Balancy Photo da ke Kano, ya yabawa shugaban kasar kan zabin Hannatu Musawa, duba da irin jajircewarta wajen gwagwarmaya, ‘ko da yake ba zan yi mamaki ba, duba daga inda ta fito, duk fadin kasar nan babu wanda bai sai mahaifinta ba kan gwagwarmaya’.

Ya kara da cewa matasa suyi kwaikwayon Farfesa Adamu abubakar gwarzo wajen taimakawa Alumma musammama akan ilimi Allah yabawa kasarmu zaman lafiya

Don haka nake kara kira ga matasa kan du daina raina sana a, musamman ta hoto, duk wani budi da Allah ya ke yiwa bawa a rayuwa hoto yayi min.

A nasa jawabin, Nasiru Rabiu wanda aka fi sani da (Tubeless) Shugaban Kamfanin Tubless Media Concept ya jaddada muhimmancin hadin kai a matsayin mabudin ci gaba a cikin kowace al’umma,

Don haka yake kara kira da yan Ƙungiyar tasu domin kara hada kai su zama tsintsiya madaurinki daya, wannan zai saka su zama abin misali.

Ya kuma kara godiya ga yadda aka Zaɓi minista Hannatu a daidai lokacin da ake bukatar masu kishi iriinta.

Daga karshe Tubeless ya jajantawa masu sana ar hoto musamman na jihar Kano kan tsada da hauhawar farashin kayan aiki da kuma bata gari da suke kutse cikin sana ar domin kassarata.

Ya jaddada cewar kungiya na kokarinta wajen hada kai da gwamnati domin kawo sauyi a sana ar.

Shi kuma Abdulwahab Blue less Shugaban Kamfanin Blue Less Multimedia ya nuna farin cikin sa, kan yadda yayan kungiyar suka yi dandazo wajen ranar masu hoto ta duniya 19th August.

Sannan yayi kira ga mataimaki na musamman ga Gwamnan Kano kan daukar hoto da yayi koyi da takwararnsa da ya gabata Aminu Dahiru wajen kawowa wannan Masana’antar ci gaba, duk abin gwamnati zata yi ya kasance an saka yayan kungiyar.

A karshe yayi ga al’umma musamman mambobinsu wajen cika alkawari da rikon Amana.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/Jmw5CBsPV6H3DbSgnlFUHM

One Reply to “Masu Ɗaukar Hoto Na Arewa Sun Magantu Kan Hannatu Ministan Fasaha Da Al’adu”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *