Daga Aminu Bala Madobi
Kungiyar kare haƙƙin ɗan Adam da ɗorewar tattalin arziki, wato SERAP, ta zargi gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da naɗa wasu mambobin jam’iyyar APC a matsayin kwamishinonin zaɓe (RECs) a hukumar INEC, da zummar taimaka masa cin zaɓe a shekarar 2027.
SERAP ta bukaci Shugaba Tinubu da ya soke nadin, inda ta ce hakan zai iya lalata amincewar al’umma da tsarin zabe a Najeriya. A cewarta, a kalla mutum uku daga cikin waɗanda aka naɗa ana zarginsu da kasancewa ‘yan jam’iyya ko kuma na kusa da jam’iyyar APC.
Wasu daga cikin waɗanda aka ambata a matsayin masu alaƙa da APC sun haɗa da:
Etekamba Umoren (Daga Akwa Ibom)
Isah Shaka Ehimeakne (Edo)
Bunmi Omoseyindemi (Lagos)
Anugbum Onuoha (Rivers)
Kungiyar ta ce, “Yin hakan barazana ce ga sahihancin zaɓuɓɓuka da kuma dimokuraɗiyya a ƙasar.”
Har ila yau, SERAP ta bukaci Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi, da ya gabatar da kudiri a gaban majalisa domin karfafa ikon INEC da tabbatar da cewa naɗe-naɗen hukumar basa karkata ga kowace jam’iyya.
A hannu guda, jam’iyyar APC ta bayyana goyon bayanta ga Shugaba Tinubu a zaɓen 2027, tana mai cewa duk da ƙalubalen tattalin arziki, ya nuna bajinta a wasu fannoni.
Ga Masu Son Bada Talla A Kira +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zN