Dimokuradiyya Na Tangal Tangal a Kawancen Tinubu Da Wike – Hadimin Tinubu da yayi Murabus

FB IMG 1742320893164

Daga Aminu Bala Madobi

Dr Aliyu Audu ya mika takardar murabus din ne ta wata wasika mai kwanan wata 8 ga watan Yuni, 2025, wanda ya mika ta ofishin shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila.

Audu, babban mataimaki na musamman kan hulda da jama’a ga shugaban kasa Bola Tinubu, ya yi murabus a hukumance, yana mai gargadi kan abin da ya bayyana a matsayin yunkurin mayar da Najeriya jam’iyya daya a karkashin jam’iyyar APC mai mulki.

Audu ya mika takardar murabus din ne ta wata wasika mai kwanan wata 8 ga watan Yuni, 2025, wanda ya mika ta ofishin shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila.

A cikin wata sanarwa da Audu ya fitar dangane da murabus din nasa, ya fayyace cewa ba wai siyasa ba ne ya sa ya yanke hukuncin, sai dai lamiri.

A yayin da yake nisanta kansa da jam’iyyar adawa ta PDP, Audu ya jaddada kin amincewarsa da matakin yunƙurin dakile muryoyin ‘yan adawa da kuma bata tsarin dimokradiyyar Najeriya.

Audu ya kuma yi gargadin illar da ke tattare da murkushe fafata harkokin siyasa, inda ya yi kira da a yi siyasa cikin girmamawa bisa akida da rikon amana.

A yayin da yake bayyana ci gaba da goyon bayan gwamnatin Tinubu na sake fasalin tattalin arzikin kasar, Audu ya bayyana rashin amincewa da kawancen siyasar da ke cikin jam’iyya mai mulki a halin yanzu, musamman alakar da ke tsakanin shugaba Tinubu da ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike.

“Mun bambanta kawai game da ra’ayoyin siyasa yayin da nake alfahari da kasancewa mai son ci gaba da kuma inganta dabi’un dimokiradiyya wanda da alama ayanzu ke tangal tangal cikin ƙawancen mara amfani na Tinubu da Wike.”

A cikin wasikar, Audu ya ce: “Na rubuta ne domin in mika takardar murabus na a matsayin babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin jama’a, nan take.

“Ina matukar godiya a gare ka, mai girma shugaban kasa, bisa damar da ka bani na yi wa kasata hidima karkashin jagorancinka mai hangen nesa. Ina mika godiya ta musamman ga Mista Ajuri Ngelale, tsohon mai ba da shawara na musamman kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a, wanda ya amince da ni duk da takaitaccen sanin da muka yi da shi ya sa aka nada ni a ranar 26 ga watan Agusta, 2023.

Ga Masu Son Bada Talla A Kira   +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zN

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *