An Kama Ɗan Majalisar Wakilai Da $500,000

Alfijr ta rawaito an kama dan majalisar wakilai da dala 500,000 tare da jerin sunayen wadanda ake sa ran za su amfana.

Jami’an ‘yan sanda da ke da alaka da rundunar ‘yan sandan jihar Ribas sun kama Chinyere Igwe, dan majalisar wakilai da kudi $498,100.

Kakakin rundunar ‘yan sandan, Grace Iringe-Koko, ta ce an kuma kama dan majalisar da jerin sunayen kudaden da za a raba.

Ta ce, “Jami’an ‘yan sanda daga jihar Ribas sun tura hedikwatar INEC, dake titin Aba a yau 24/2/2023 da misalin karfe 0245 na safe, yayin da suka tsaya ana bincike, sun kama wani dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar tarayya ta Fatakwal II, Honourable Chinyere Igwe. tsabar kudi $498,100 a cikin jaka cikin motarsa,” kamar yadda kakakin ‘yan sandan ta rubuta a cikin wata sanarwa.

“Haka kuma da aka gano akwai jerin sunayen da za a raba kudin.” Iringe-Koko ya ce Abutu Yaro, mataimakin sufeto-janar (zaben) ya ba da umarnin “yi gaggawar yi wa dan majalisar tambayoyi sannan kuma a gurfanar da shi a gaban kotu.

Ƴan sanda sun bukaci dukkan ‘yan takara da jam’iyyun siyasa da su bi daidai da tanade-tanaden Dokar Zabe na 2022 da sauran dokokin da ke jagorantar zabuka.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/KrigvNKcneVBHxctLUQ0ux

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *