Alfijr ta rawaito ƴan bindiga da ake zargin ‘yan daba ne sun kai hari kan matar dan takarar gwamna a jam’iyyar PDP a jihar Zamfara, Dauda Lawal Dare lamarin da aka ce ya faru a Gusau.

An ce ya hada da matar Dare, mataimakanta, da sauran masu wucewa marasa laifi.
Dare wanda ya bayyana hakan ga manema labarai a lokacin da yake ganawa da manema labarai a gidansa.
Ya bayyana cewar harin ya yi sanadin jikkata wasu mutane daban-daban.
Ya yi zargin cewa gwamnati ce ta dauki nauyin kai harin, yana mai cewa harin ya faru ne sakamakon farin jinin siyasar da jam’iyyar PDP ta samu a jihar kawo yanzu.
“Na riga na kai rahoton mummunan ci gaban da aka samu ga hukumomin tsaro a jihar, ina jiran martanin su”, in ji shi.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇