Alfijr ta rawaito Gwamnan jihar Kano mai barin gado, Dr Abdullahi Umar Ganduje ya gamu da cikas a bukin rantsar da sabon shugaban kasa a Eagle Square da ke Abuja.
Ganduje da matarsa Hafsat sun yi kokarin shiga cikin wurin da ake kebe wa manyan baki masu alfarma amma sai jami’an tsaro suka dakatar da shi suka ce takardar gayyatar da yake da ita koriya ce kuma sai mai takardar gayyata mai ruwan gwal ne zai shiga cikin wannan bangaren.

Ya jira na tsawon fiye da minti 10 kafin ya dauki kaddara ya koma bangaren da aka tanadar wa baki irinsa.
Shi ma gwamnan jihar Anambra, Charles Soludoya yi kokarin shiga wannan bangaren amma kamar Ganduje shi ma jami’an tsaro sun taka masa birki.
BBC
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ
𝐀𝐥𝐥𝐚𝐡 𝐦𝐚𝐢𝐦𝐚𝐢 𝐝𝐚 𝐛𝐚𝐰𝐚 𝐝𝐚, 𝐉𝐢𝐲𝐚 𝐠𝐰𝐚𝐦𝐧𝐚 𝐲𝐚𝐮 𝐭𝐬𝐨𝐡𝐨𝐧 𝐠𝐰𝐚𝐦𝐧𝐚,
Good afternoon every one