Alfijr ta rawaito an rantsar da Injiniya Abba kabir Yusuf a matsayin sabon gwamnan Jihar kano, a bikin da aka yi a filin wasa na Sani Abacha da ke Kofar Mata a birnin Kano.
An rantsar da shi tare da mataimakinsa Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo.
Dubun dubatar magoya bayan jam’iyyar NNPP ne sanye da fararen kaya da jajayen huluna ga maza yayin da mata ke sanye da jajayen dan-kwali ko mayafi ko hijabi a wurin taron.

Sarakunan jihar ta Kano da jagoro kuma dan takarar jam’iyyar ta NNPP Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da sauran manyan baki ne suka halarci bikin.
Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP ya yi nasara ne a zaben da aka yi ranar 18 ga watan Maris inda ya kayar da dan takarar jam’iyya mai mulki, APC, Nasiru Yusuf Gawuna.
BBC
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ
𝐀𝐥𝐥𝐚𝐡 𝐲𝐚𝐢 𝐫𝐢𝐤𝐨 𝐝𝐚 𝐡𝐚𝐧𝐧𝐚𝐲𝐚𝐧𝐬𝐚,