Buhari ya Naɗa Sha’aban Sharada Shugaban Hukumar Kula Da Almajirai


Alfijr ta rawaito Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya nada ɗan majalisar Karamar Hukumar Binnin Jihar Kano mai barin gado Sha’aban Ibrahim Sharada matsayin sabon kwamishinan hukumar kula da Almajirai ta Kasa.

Cikin wata Sanarwa da Mataimakawa Shugaba Buhari kan yada Labarai Malam Garba Shehu ya fitar ta taya Hon Sha’aban Sharada  murna.

Sha’aban Ibrahim Sharada ya yiwa Jam’iyar ADP takarar Gwamnan Jihar Kano a Zaben 2023.

Nadin nasa dai na zuwane awannin kadan kafin karewar wa’adin mulkin shugaban Kasa Muhammadu Buhari.

Matashin  ya kammala Digirinsa na farko a jami’ar Bayero Dake Kano a fannin  Aikin Jarida inda yayi Digirin Digirgir a fannin Gudanarwa a jami’ar Chichester Dake birnin Landan.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijr Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 

https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *