Alfijr ta ra rawaito Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Bauchi, SEMA, ta tabbatar da mutuwar mutane 10 sakamakon ambaliyar ruwa da ta lalata gidaje da gonaki da dama a fadin jihar.
Alfijr Labarai
Daraktan tsare-tsare, bincike da kididdiga a hukumar Adams Nayola, ya tabbatar da hakan a wata hira da Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN a yau Laraba a Bauchi.
Ya ce lamarin ya tilastawa mazauna yankin samun mafaka a wasu wurare Cavan daban
Adams kara da cewar, hukumar na ci gaba da tattara bayanai kan filayen noma da gidajen da su ka lalace a faɗin jihar.
“Akalla mutane 10 ne suka rasa rayukansu yayin da ya tafi da hektoci da dama na gonaki da gidaje a wasu sassan jihar.
Alfijr Labarai
“Kananan hukumomin da abin ya fi shafa sun hada da Jama’are, Giade, Misau, Dambam, Zaki, Darazo, Kirfi, Itas-Gadau, Shira, Gamawa da Toro.
“Duk da cewa ambaliyar ta shafi kananan hukumomi 19 cikin 20 na jihar Bauchi, matsalar ta fi ƙamari a kananan hukumomi goma sha biyu ne kawai,” in ji Nayola.