Alkalla Mutane 25 Sun Mutu Sakamakon Hatsarin Kwale-Kwale Daban-Daban a Najeriya

FB IMG 1723210844046

Daga Aminu Bala Madobi

Akalla mutane 25 ne suka mutu a wasu hadurran kwale-kwale a jihohin Jigawa da Bayelsa.

Rahotanni daga karamar hukumar Taura ta jihar Jigawa na cewa, a jiya wani jirgin ruwa dauke da fasinjoji dake tsallaka kogin Gamoda a kauyen Nahuce ya kife, inda mutane 5 suka mutu, wasu 15 kuma suka bace

Kazalika akalla mutane 20 ne suka mutu bayan da wani kwale-kwalen katako ya kama da wuta bayan ya yi bindiga a wani kogi a jihar Bayelsa da ke gabar tekun Najeriya a ranar Laraba, in ji kakakin ‘yan sandan.

Kwale-kwalen dai na dauke da ‘yan kasuwa ne da ke kai kayayyaki zuwa yankunan bakin teku, kamar yadda kakakin rundunar ‘yan sandan Bayelsa Musa Muhammed ya bayyana a ranar Alhamis.

‘Yan kasuwa kan yi tafiye-tafiye na mako-mako tsakanin matsugunan bakin teku da Yenagoa babban birnin jihar.

Akalla dai mutane 200 ne aka rawaito sun rasa rayukansu a hatsarin kwale-kwale a Najeriyar a bara, inda hukumomi kan dora alhakin hakan akan cunkusa mutane da rashin kula da matakan kare aukwar hadurra.Reuters

Sharhi TV

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *