Jami’ar Bayero Kano ta shiga jerin manyan jami’o’in duniya na shekarar 2026.

Screenshot 20240302 154602 com.android.chrome edit 2469728761081

Wannan na zuwa ne bayan da kasar ta kafa wani tarihi a fannin ilimin  jami’o’i in da 24 suka samu gurbi a jerin manyan jami’o’in duniya na  shekara ta 2026 da mujallar Times Higher Education (THE) ke fitarwa.

Hakan ta sa Najeriya ta zama ƙasar da ta fi kowacce yawan jami’o’in da suka shiga wannan jerin a yankin Afirka.

A cikin jerin, Jami’ar Ibadan da Jami’ar Legas ne suka kasance a sahun gaba a Najeriya, yayin da Jami’ar Bayero ta zama ta uku  daga cikin jami’o’in da suka fi nuna ƙwazo.

Adadin jami’o’in Najeriya da suka shiga jerin ya ƙaru daga 21 a shekara ta 2024 da 2025 zuwa 24 a shekara ta  2026.

Jami’o’in da suka shiga jerin sun haɗa da jami’o’in gwamnatin tarayya guda 17, da na jihohi guda uku da kuma jami’o’i masu zaman kansu guda huɗu.

Masana sun ce hakan na nuna ci gaban da ake samu a fannonin koyarwa da  bincike da ƙirƙire-ƙirƙire da kuma alaƙar ilimi da ƙasashen duniya.

Har ila yau, wasu jami’o’in fasaha da na aikin gona sun samu gurbi a jerin, lamarin da ke nuna yadda waɗannan cibiyoyin ke ƙara samun karɓuwa a matakin duniya.

Da yake martani kan wannan nasara, ministan Ilimi Dakta Tunji Alausa, ya ce hakan wata babbar nasara ce ga ilimin jami’o’i, yana mai nuna irin tasirin gyare-gyaren da gwamnati ke aiwatarwa domin inganta jami’o’in Najeriya.

Ya ƙara da cewa samun wannan karɓuwa a duniya zai taimaka wajen ƙara haɗin gwiwa da jami’o’in ƙasashen waje, samun tallafin bincike, da kuma ƙarfafa saka hannun jari a harkokin koyarwa, bincike da bunƙasa jami’o’i.

Jami’o’in  24 da suka shiga jerin sun haɗa da:

1. Jami’ar Ibadan

2. Jami’ar Legas

3. Jami’ar Bayero Kano

4. Covenant University

5. Landmark University

6. Jami’ar Ahmadu Bello

7. Jami’ar Fasaha ta Tarayya, Minna

8. Jami’ar Ilorin

9. Jami’ar Jos

10. Jami’ar Najeriya, Nsukka

11. Babcock University

12. Jami’ar Jihar Delta, Abraka

13. Jami’ar Jihar Ekiti

14. Jami’ar Aikin Gona ta Tarayya,

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *