Gwamnan Kano ya raba kyautar filaye ga masu rike da mukami su 300

FB IMG 1778588658214

Gwamnan Jihar Kano, Abba Yusuf, ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta yi aiki tukuru domin tabbatar da nasarar Shugaba Bola Tinubu da jam’iyyar APC a zaɓen shekarar 2027.

Gwamna Abba  ya bayyana hakan ne yayin wani taro da zaɓaɓɓun jami’ai da naɗaɗɗun masu riƙe da muƙaman gwamnati a gidan gwamnati da ke Kano, inda ya ce jihar za ta jagoranci tattara ƙuri’u masu yawa ga Tinubu.

Gwamnan ya umarci dukkan masu riƙe da muƙaman gwamnati da ba su yi rajista a APC ba da su gaggauta yin hakan, yana mai cewa dole ne jami’an gwamnati su taimaka wajen ƙarfafa jam’iyyar kafin zaɓen 2027.

Ya kuma jaddada aniyar gwamnatinsa na ganin APC ta yi nasara a zaɓen shugaban ƙasa, gwamna, majalisun dokoki da ƙananan hukumomi.

A wani mataki na ƙarfafa gwiwar masu riƙe da muƙaman siyasa, gwamnan ya amince da rabon filaye ga fiye da mataimaka 300 tare da ba kowane ɗaya daga cikinsu tallafin naira 100,000.

Shi ma Kakakin Majalisar Dokokin Kano, Ismail Falgore, ya ce APC na da dalilan tallata ayyukan Shugaba Tinubu ga al’ummar jihar, yayin da shugaban APC na Kano, Umar Haruna Doguwa, ya ce jam’iyyar ta shirya tsaf domin zaɓen 2027.

Sanarwar ta ƙara da cewa mahalarta taron sun amince da ƙuri’ar amincewa ga Shugaba Tinubu da Gwamna Yusuf tare da yin alƙawarin ƙara wayar da kan jama’a domin tabbatar da nasarar APC a zaɓen 2027.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *