DSS ta biya wani mutumi diyyar N3m bayan kuskuren kama shi kan zargin alaƙa da ta’addanci

IMG 180130 28626 1782666108439

Hukumar Tsaron Farin Kaya ta Najeriya (DSS) ta saki wani manomi ɗan asalin Jihar Kaduna, tare da wanke shi daga zargin alaƙa da ƙungiyar Boko Haram, sannan ta biya shi diyyar naira miliyan uku.

Shugaban hukumar DSS, Oluwatosin Adeola Ajayi, ne ya bayar da umarnin sakin mutumin, Nura Idris, wanda manomi ne kuma makiyayi daga Ƙaramar Hukumar Soba ta Jihar Kaduna, yayin da ake ci gaba da nazarin batutuwan waɗanda aka tsare ba bisa ƙa’ida ba.

Majiyoyin tsaro sun ce binciken cikin gida da DSS ta gudanar ya tabbatar da cewa babu wata alaƙa tsakanin Nura da mayaƙan Boko Haram.

Majiyoyin sun ce wata hukumar tsaro ce ta kama Nura a watan Yunin 2024 a garin Suleja da ke Jihar Neja, kafin daga bisani ta miƙa shi ga DSS bisa zargin yana da alaƙa da ta’addanci.

Bayan cikakken bincike kan lamarinsa, DSS ba ta samu wata hujja da ke danganta shi da ta’addanci ba.

Bisa haka ne shugaban hukumar ya ba da umarnin a sake shi nan take, tare da amincewa a ba shi naira miliyan uku a matsayin diyya domin tallafa masa wajen komawa cikin iyalansa ya kuma sake gina rayuwarsa.

Haka kuma, ya yi masa alƙawarin ƙarin tallafi domin ya sake dogaro da kansa.

Da yake magana bayan an sake shi, Nura Idris ya nuna godiyarsa ga DSS, inda ya bayyana hakan a matsayin wani abu da zai sauya rayuwarsa.

Ya kuma yaba da kyakkyawar kulawar da ya samu yayin da yake tsare kamar yadda majiyoyin tsaro suka ambato.

Baya ga Nura, DSS ta kuma sake nazarin tuhume-tuhume fiye da 30, tare da biyan diyyar sama da naira miliyan 300 ga mutanen da aka tsare ba bisa ƙa’ida ba.

Daga cikin mutanen da aka saki akwai waɗanda a baya aka zarge su da alaƙa da haramtacciyar Ƙungiyar Fafutukar Kafa Ƙasar Biafra (IPOB) da sauran ƙungiyoyin da ake zargi da ta’addanci, bayan bincike ya tabbatar da cewa ba su da laifi.

DSS ta bayyana cewa wannan shiri yana nuna aniyarta ta daidaita ayyukan tsaro da kare haƙƙin ’yan ƙasa, tare da ƙara ƙarfafa amincewar jama’a ga hukumomin tsaron ƙasar.

Trust Radio

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *