Fata Na Gari: Ana hasashen farashin fetur zai sauka zuwa N900 idan sulhun Amurka da Iran ya kammala

FB IMG 1781537494873

Masu harkar man fetur a Najeriya sun bayyana cewa farashin fetur na iya sauka zuwa kusan N900 kan kowace lita idan yarjejeniyar sulhu tsakanin Amurka da Iran ta tabbata tare da ci gaba da raguwar farashin danyen mai a kasuwar duniya.

Rahotanni sun nuna cewa farashin danyen mai ya ragu daga sama da dala 120 kan ganga a watan Afrilu zuwa kusan dala 87, lamarin da ya haifar da fatan cewa farashin fetur, dizal da man jiragen sama zai sauka.

A lokacin rikicin Amurka da Iran, farashin fetur a Najeriya ya tashi daga kusan N830 zuwa N1,300 kan lita sakamakon tashin farashin danyen mai. Sai dai yanzu da ake sa ran sake bude mashigar ruwa ta Hormuz da kuma dawowar zaman lafiya, masu kasuwancin man fetur na ganin farashin zai iya komawa kasa.

Jaridar Punch ta rawaito cewa, wata majiya daga Matatar Man Dangote ta bayyana cewa duk da cewa har yanzu matatar na da danyen mai da ta saya a farashi mai tsada, akwai yiwuwar farashin fetur ya sauka zuwa N900 idan raguwar farashin danyen mai ta ci gaba.

Shi ma Sakataren yada Labarai na kungiyar masu gidajen mai ta PETROAN, Joseph Obele, ya ce idan aka sake bude mashigar Hormuz, farashin fetur zai iya sauka kasa da N1,000 kan lita, yana mai tunatar da cewa kafin rikicin Gabas ta Tsakiya fetur yana sayarwa kusan N800 kan lita.

A gefe guda, Shugaban Amurka, Donald Trump, ya sanar da cewa ana sa ran rattaba hannu kan yarjejeniyar sulhu da Iran, wanda zai ba da damar bude mashigar Hormuz ga dukkan jiragen ruwa.

Masu ruwa da tsaki a bangaren makamashi sun yi hasashen cewa idan yarjejeniyar ta yi nasara kuma farashin danyen mai ya ci gaba da sauka, za a iya ganin sabon zagayen rage farashin fetur a Najeriya cikin kwanaki masu zuwa.

Daily Nigerian

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *