Ma’aikatar Muhalli da Sauyin Yanayi ta jihar Kano ta ƙaddamar da kundin dokokin tsaftar muhalli da ta fassara da harshen Hausa.
Kwamishinan ma’aikatar, Dakta Dahir Muhammad Hashim ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a jiya Laraba a Kano.
Ya ce an fassara kundin dokoki da kuma kundin ƙa’idojin kula da gurɓatar muhalli ne domin “sauƙaƙa fahimta da kuma cigaba da wayar da kan jama’a akan dokokinmu na tsaftar muhalli”
Hashim ta baiyana cewa tun a watan Afrilu ya ɗauki alƙawari cewa za a fassara su zuwa harshen Hausa.
“Yau, cikin yardar Allah, ina sanar da ku cewa mun kammala wannan aikin tare da samar da cikakkun kundin da kowa zai iya saukewa kai tsaye tare da na turancin su,” in ji Kwamishinan..
Kundin sun haɗa da – Kundin Dokar Kula da Gurɓatar Muhalli ta Jihar Kano, 2022 (Kano State Environmental Pollution Control Law 2022)
Da kuma Ƙa’idodin Kula da Gurɓatar Muhalli da Shawo kan Shara ta Jihar Kano, 2025 (Kano State Environmental Pollution and Waste Control Regulations 2025).
Ya kuma ce za a iya samun waɗannan kunshe ta yanar gizo akan adireshin https://environment.kn.gov.ng/resources
“Ina kira ga duk masu ruwa da tsaki da su karanta su kuma bi wadanan dokoki da ƙa’idodi domin rashin sani ba zai zama hujja ba,” in ji shi.


Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD