Shugaban Najeriya Bola Tinubu zai kawo ziyara Kano a yau juma’a

IMG 090235 18725 1752825775442

Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu zai zo Kano ranar Juma’at nan 18 ga watan yuli

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Mai magana da yawun gwamnan Kano Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar

Sanarwar ta ce shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu zai kawo ziyayarar ne domin yin ta’aziyyar marigayi Alhaji Aminu Alhassan Dantata wanda ya rasu a baya bayan nan.

Sanarwar Ta kuma bukaci al’ummar jihar kano da su kasance masu karamci kamar yadda suka saba wajen nuna dattako da karbar bakuncin Shugaban kasar a gobe juma’a.

Tun bayan Rasuwar Marigayi Alhaji Aminu Dantata Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu bai samu damar zuwa Kano ba, Sai Gobe, amma dai Mataimakin sa Kashim Shettima ya zo amadadinsa.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *