Budaddiyar Wasika Ga Gwamnatin Kano Kan Matsalar Matatar Ruwa Ta Tamburawa (CLARIFIER WATER WORKS.)

Abba k Yusuf

Assalamu alaikum warahmatullah wabarakatuhu

Cikin girmamawa da biyayya muke maka fatan alheri mai girma Gwamna Alh Abba Kabir Yusuf

Mai girma Gwamna mun sanka da jin koken al’umma mutukar sun koka akan duk wata matsala da ta dame su don haka muke amfani da wannan kafa domin isar maka da sakon mu duba da bamu da hanyar zuwa wajenka sai ta nan.

Muna kira da girmamawa ga Gwamn Kano da ya duba matsalolin da ke addabar Tamburawa Clarifier Water Works.

Fiye da watanni shida, muke da matsalar ruwan sha — kamar Gyadi-Gyadi, Hausawa, Tudun Maliki da sauran unguwanni — mun dade muna fama da ƙatsewar ruwan sha gaba ɗaya.

Wannan dogon lokaci na rashin ruwa mai tsafta ya jefa jama’a cikin ƙunci, inda mutane ke dogaro da ruwan da ba ya da tsabta ko tabbas, wanda hakan ke da mummunan tasiri ga lafiya da walwalar al’umma.

Muna roƙon gwamnati da ta tausayawa halin da muke ciki, ta kuma ɗauki matakin gaggawa domin dawo da ruwan sha a yankunanmu.

Allah ya taimaki Gwamna aka ayyukan alheri da yake bijiro mana dasu a fadin jihar ameen.

Sa’idu Husain Abdullahi.
Mazaunin Tudun Maliki/ Gidan Zoo, Kano.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *