Gwamnatin tarayyar Najeriya, ta ayyana ranakun hutun bukukuwan babbar Sallah (Eidul Adha).
Ministan harkokin cikin gida na kasar, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya sanar da hakan ta cikin wata sanarwa da babban Sakataren ma’aikatar, Dakta Magdalene Ajani, ya fitar a yau Litinin, inda ya ce ranakun hutun sune Jumu’a 6 ga watan Yuni da kuma Litinin 9 ga watan Yunin shekarar 2025.
A cewar Ministan, “Ina tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa sauye-sauyen da suka shafi jin daɗin al’umma da ake aiwatarwa a ƙarƙashin shirin “Sabunta Fata” na Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, na kokarin kai Najeriya kan turbar ci gaba”.
A karshe Ministan ya taya al’ummar Musulmi murnar bikin babbar sallar, inda ya buƙaci ‘yan kasar da su hada mai da gwamnati wajen kokarin dawo da martabar Najeriya a matsayin ƙasa mai girma.
Ga Masu Son Bada Talla A Kira +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zN