Rasuwar Matasa 21 Da Suka Wakilci Kano Wani Babban Gibi Ne Mai Wuyar Cikewa – Sarki Aminu Bayero

FB IMG 1709422107907

Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya bayyana alhininsa da samun labarin rasuwar Yan wasan da suka wakici jihar Kano a Gasar wasanni ta kasa da aka gudanar a garin Abekuota dake jihar Ogun.

A safiyar yau ne dai Asabar aka tashi da hatsarin motor data dakko Yan wasan inda sakamakon fadawar motar cikin wani rami, Yan wasan su 21 suka rasu wasu Kuma suka jikkata.

Hatsarin dai ya faru ne a garin  Dakatsalle dake yankin karamar Hukumar Garun Malam anan jihar Kano gab da karasowarsu cikin birnin Kano.

Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya bayyana rasuwar matasan da cewa wani babban rashi ne bawai ga iyalansu ba harma da al’umar jihar Kano baki daya.

Yayi addu’ar Allah ya jikansu ya gafarta musu ya Kuma baiwa iyalansu hakurin jure wannan babban rashi yasa aljanna makoma a garesu.
Haka kuma mai martaba sarki yayi addu’ar wadanda suka samu raunuka.Allah ya tashi kafadunsu.

Sa hannu
Abubakar Balarabe Kofar Naisa.
Sakataren Yada labarai na Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero CFR JP CNOL

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ga Masu Bada Talla Zasu Iya kiran+2348032077835

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *