Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya bayyana alhini kan mummunan hatsarin mota da ya yi sanadin mutuwar matasa 22 daga cikin tawagar ‘yan wasan Jihar Kano, tare da jikkatar wasu da dama.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a ranar Asabar, 31 ga Mayu, 2025 gwamnatin Kano ta ayyana Litinin, 2 ga Yuni, a matsayin hutun aiki a fadin jihar domin bai wa al’umma damar yin addu’o’i da jimami ga mamatan da iyalansu.
Gwamnan, wanda ke kasa mai tsarki domin gudanar da aikin Hajji, ya yi kira ga limamai da daukacin al’ummar Musulmi da su yi da addu’o’i domin neman gafara da rahamar Allah ga wadanda suka rasu, tare da rokon Ubangiji Ya bai wa iyalansu hakuri da juriya a wannan ibtila’i i.
Gwamnatin Abba bayyana hatsarin a matsayin babban rashi ga jihar da ma kasa baki ɗaya, inda ta jaddada kudirinta na ci gaba da tallafa wa wadanda suka jikkata da kuma iyalan mamatan.
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ga Masu Bada Talla Zasu Iya kiran+2348032077835
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD